Asalin hoton, EPA
- Marubuci, Yasmine Shahine
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Arabic
- Aiko rahoto daga Cairo
Masar da wasu ƙasashen Larabawa na aiki kan shirin sake gina Gaza wanda zai tabbatar da Falasɗinawa sun cigaba da zama a yankin ba tare da an fitar da su ba, da kuma samar da tsarin shugabaci a Zirin ba tare da sa hannun Hamas ba.
Hakan na zuwa ne bayan shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana shirinsa na mayar da Falasɗinawa zuwa Masar da Jordan da kuma wasu ƙasashen, da kuma karɓe iko da Gaza domin mayar da yankin abin da ya kira ''ƙayataccen wuri a Gabas ta Tsakiya''.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa aƙalla ƙuduri huɗu aka rubuta kan Gaza, amma ƙudurin Masar ne ake ganin ƙasashen Larabawa za su yi amfani da shi a madadin shirin Trump.
A cewar majiyar BBC, Masar na dab da kammala tsara shirin wanda ya haɗa da kwashe ɓaraguzan gine-ginen, sake gina Gaza, tsara yadda Falasɗinawa za su rayu a wannan lokacin da kuma samar da tsarin gwamnati bayan yaƙin.
Sai dai har yanzu ana cigaba da tattauna makomar ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai kamar su Hamas da Islamic Jihad.
Masar ta ce za a bunƙasa shirin tare da haɗin gwiwar gwamnatin Amurka.
Majiyoyi daga Masar sun shaida wa BBC cewa Majalisar ɗinkin duniya da Tarayyar Turai za su taka rawa a cikin shirin.
Masar na shawartar ƙasashen Larabawa da dama kamar Jordan da Saudiyya kan shirin, gabanin taro yanki da za a yi a Riyadh a ranar 21 ga watan Fabarairu, wanda mai yiwuwa za a yi tare da hukumomin yankin Falasɗinawa.
Bayan wannan taron, za a yi taron gaggawa na ƙasashen Larabawa a birnin Alƙahira wanda tun da farko aka shirya yin sa a ranar 27 ga watan Fabarairu kafin a ɗage shi saboda wasu dalilai kuma ba tare da sanya sabuwar ranar yinsa ba.
Asalin hoton, Reuters
Ta yaya za a aiwatar da shirin ba tare da an tashi Falasɗinawa ba?
Wata majiya daga Masar ta shaida wa BBC cewa tuni aka fara shawarwari tsakanin ƙasashen Larabawa domin shirya babban taro da za a yi nan gaba kan sake gina Gaza wanda ƙasashen Turai za su halarta.
Majiyar ta kuma ƙara da cewa shirin Masar ya mayar da hankali ne kan sake gina Gaza da kuma raba Zirin zuwa yankunan jin-ƙai uku, wanda za a kafa manyan sansanoni 20 domin mutane su zauna a ciki, kuma za a samar musu da ababen more rayuwa kamar ruwa da wutar lantarki.
Kamar yadda tsarin yake, za a samar da dubban gidaje da rumfuna a yankunan da akwai tsaro na watanni shida, a lokaci guda kuma za a kawar da ɓaraguzan gine-gine da aka samu sakamakon yaƙin.
Sai dai Isra'ila ba ta amince da hakan a yanzu ba da ake matakin farko na yarjejeniyar tsagaita wuta.
Shrin zai kuma jaddada buƙatar barin shigar da man fetir da kayyaykin gini cikin Gaza a kai a kai.
A cewar shirin na Masar, ƙasashen larabawa da wasu ƙasashen duniya ne za su tara kuɗaɗen da za a sake gina Gaza, wanda kamfanoni 50 da su ka kware a gine gine za su samar da rukunin gidaje cikin watanni 18 a yankunan Gaza uku da aka tsara.
Hakazalika wani kwamiti da ya haɗa da larabawa da wakilai daga ƙasashen waje ne za su kula da asusun.
Shirin ya kuma haɗa da samar da tudun mun tsira da kuma sanya wani shinge domin daƙile haƙar hanyar ƙarƙashin ƙasa a kan iyakar Gaza da Masar, sai kuma kwashe ɓaraguzai da kuma samar da rukunin gidajen wucin gadi 20 a arewaci, tsakiya da kuma kudancin Zirin.
Dakta Tarek al-Nabarawi, shugaban ƙungiyar injiniyoyin Masar ya shaidawa BBC cewa shirin zai iya shafe shekaru 3 zuwa biyar ana yi, idan akayi la'akari da ƙasashe nawa ne za su sa hannu ciki da kuma kuɗin da za a buƙata.
Sai dai a ranar asabar, Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya bayyana cewa ba zai bari a shigar da gidajen wucin gadi da kayyayakin gine gine cikin Gaza ba, inda ya ce saboda dalilan tsaro, duk da dai hakan na cikin yarjejeniya tsagaita wuta na baya bayan nan.
Asalin hoton, Getty
Makomar Hamas
Wata majiya daga Masar ta shaidawa BBC cewa abu mafi muhimmanci shi ne makomar ƙungiyar Hamas da kuma sauran ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai da ke Zirin Gaza.
Majiyar ta bayyana cewa ɗaya daga cikin shirye shiryen Masar ɗin ya haɗa da waɗannan ƙungiyoyin su ajiye makaman su da zarar an ayyana ƙasar Falasɗinawa cikin iyakokin da ake da su kafin yaƙin kwananki shida.
Gabashin birnin kudus zai kasance babbar birnin wannan ƙasar kuma za a samar da Tudun mun tsira- a wani wuri da ba a riga an tantace ba- domin tabbatarwa Isra'ila cewa wata barazana ba zata fito daga Gaza ba.
Shirin kuma zai haɗa da kafa wani kwamitin Falasɗinawa da zai shugabanci Gaza ba tare da sa hannun Hamas ba.
Dakarun ƙasahen larabawa da na wasu ƙasashen duniya za su taimaka wa kwamitin kula da Zirin Gaza na wani ɗan lokaci.
Tun a baya Hamas ta ce ta shirya barin wa kwamitin ƙasa shugabancin Gaza, amma ta na son ta taka rawa wajen zaɓen mambobin kwamitin, haka kuma ba zasu amince da turo wasu dakaru ba ba tare da amincewarsu ba.
Majiyar daga Masar ta kuma jaddada cewa bisa shirin, ƙasashen larabawa za su taimakawa hukumomin yankin Falasɗinawa horar da jam'iansu tare da haɗin gwiwar Tarayyar Turai.
Ya batun shirin Trump?
Shugaban Amurka ya nanata shirinsa na sake wa Falasɗinawa matsuguni daga Gaza, inda ya ce hakan abu ne mai kyau saboda dama ce da zai mayar da Gaza wajen ziyarar buɗe ido kuma zai amfani Falasɗinawa ganin cewa za su daina rayuwa cikin ɓaraguzai.
Trump ya kuma yi barazanar dakatar da tallafi zuwa Masar da Jordan ida ba su karɓi Falasɗinawa ba.
Dan Perry, tsohon Editan kamfanin dillacin labarai na AP kan Gabas ta Tsakiya da ke Cairo, ya wallafa cewa shirin Trump na fitar da Falasɗinawa daga Gaza wata dama ce na matsawa ƙasashen larabawa da Falasɗinawa da ke Gaza su kawar da Hamas daga mulki.
Sai kuma dakatar da tallafin kuɗi zuwa Hamas daga ƙasashen Larabawa musamman Qatar.
Bayan wani taro a baya-bayan nan a birnin Washigton tsakanin Trump da Sarki Abdullah na biyu na Jordan, mai magana da yawun shugaban Amurka, Caroline Levitt, ta ce Sarki Abdullah ya bayyana wa Trump ƙarara cewa ya fi son Falasɗinawa su ci gaba da kasancewa a Gaza a lokacin da ake gina Gazan.
A hukumance, har yazu Trump ya fi son ya fitar da Falasɗinawan daga Gaza.
Perry na ganin cewa Trump zai iya amincewa Falasɗinawa su cigaba da kasancewa a Gaza idan Amurka za ta samu maƙudan biliyoyin dala tare kuma da tabbacin cewa za a kawar da Hamas daga yankin.
Perry na kuma ganin za a iya kafa gwamnatin farin hula a Gaza da ke da alaƙa da hukumomin yankin Falasɗinu da ke gaɓar yamma, da kuma haɗin gwiwa da Masar da ƙasashen Gulf.
Asalin hoton, Reuters
Mene ne a tsakanin Trump da Gabas ta tsakiya?
Dr Mubarak Al-Ati, wani mai sharhi kan siyasa a Saudiyya, na ganin cewa sanya hannun Amurka a wurin gina Gaza zai faru ne sanadiyyar muradan da Amurka ke da su a yankin, musamman a kan Saudiyya da Masar.
Ya ƙara da cewa alaƙar da ke tsakanin jagororin Masar da Amurka da kuma Saudiyya za ta ba su damar samun matsaya ɗaya, musamman idan aka yi la'akari da ziyarar da Trump ke shin kaiwa Saudiyya, lamarin da ake sa ran zai iya sauya fasalin alaƙar Amurka da Gabas ta tsakiya a nan gaba.
Dakta Hassan Mneimneh, mai fashin baƙi kan harkokin siyasa daga Washington na ganin cewa idan Trump ya dakatar da tallafin soji da na tattalin arziƙi zuwa Masar da Jordan a matsayin martani ga wani shirin ƙasashen larabawa, ƙasashen su mayar da martani.
A misali Riyadh ta dakatar da zuba hannun jarinta a Amurka wanda hakan zai buɗe kofar haɗin gwiwar kasuwanci da China da Rasha da Tarayyar Turai da Afirka da kuma kudancin Amurka.
Majiyar ta Masar da ba a ambaci ko wane ne ba ta bayyana cewa alamar da Masar ta nuna a bayanan na soke yarjejeniyar zaman lafiya na Camp David da aka yi da Isra'ila a 1979 zai iya tasiri kan Amurka idan Trump ya ki amincewa da shirin ƙasashen Larabawa nan gaba.